A bayanin da mahukuntar kasar ta Niger suka fitar,asibitin zai zama mafi girma kuma mai dauke da kayayyakin aiki na zamani a kasar.
Shi dai wannan biki ya samu halarta manyan kusoshin gwamnati,'yan majalissun dokoki da wakilan kasashen waje dake Niger.
Aikin gina asibitin da Kasar Sin zata yi zai bukaci kudi akalla sefa biliyan 27 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 55.8,abinda ya sa ministan kiwon lafiya na kasar ta Niger Manou Agali ya mika cikakkiyar godiyar kasar sa ga kasar Sin bisa ga taimakon da take basu tare da alkawarin tabbatar da ganin aikin ya cimma nasara.
Wassu jami'ai na ganin cewa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ya bunkasa cikin sauri musamman a bangaren siyasa, tattalin arziki, makamashi, al'adun gargajiya, tsaro da kuma samar da ababen more rayuwa. (Fatimah Jibril)