A matsayinsa na shugaban MNSD-Nasara, jam'iyyar adawa mafi girma a Nijar, Mr. Oumarou ya gana da shugaba Issoufou a fadar shugaban dake birnin Yamai. A lokacin da yake hira da manema labarai, malam Seyni Oumarou ya nuna cewa, a makon da ya gabata ne shugaba Issoufou ya riga ya nuna aniyarsa ta kafa gwamnatin hadin gwiwa. Ta haka a yayin wannan ganawa mista Oumarou ya gabatar wa shugaban kasar Nijar matsayin kawacen adawa na ARN.
Tun bayan Issoufou ya lashe babban zaben kasar Nijar a watan Maris na shekara ta 2011, akwai babban sabani a tsakanin jam'iyyun siyasa daban daban na kasar. A ranar 5 ga wata, Hama Amadou, shugaban majalisar dokokin kasar kuma shugaban Jam'iyyar LUMANA dake cikin kawancen dake mulki na MRN ya yi kira a gun bikin rufe taro karo na biyu na majalisar dokokin kasar ga jam'iyyu daban daban da su hada kai domin kare kasa da kafa gwamnatin hadin gwiwa, a kokarin magancen yunkurin kawo wa kasa baraka da makwabciyarta Mali ke fuskanta.(Kande Gao)