Sin za ta kafa tsarin bincike kan illar da gurbatacciyar iska ke haddasawa ga lafiyar al'umma

Ranar 28 ga wata, kwamitin kula da harkokin kiwon lafiya da kayyade haihuwa na kasar Sin, ya gabatar da "shirin aiwatar da bincike kan illar da gurbatacciyar iska ke haddasawa ga lafiyar al'umma na shekatar 2013", inda ya bayyana cewa, nan da shekaru 3 zuwa 5 masu zuwa, za a kafa wani tsarin bincike kan illar da gurbatacciyar iska ke haddasawa ga lafiyar al'umma a dukkanin fadin kasar Sin.
Bisa wannan shiri, an ce, a bana, za a fara aikin bincike kan illar da gurbatacciyar iska ke haddasawa ga lafiyar mutane a wasu wurare na larduna 16, wadanda suka fi fama da matsalar gurbatacciyar iska. Binciken da za a yi ya hada da nazari kan yawan mutuwar mutane, da kuma hadurran da su ke shafar lafiyar mutane, irin wadanda gurbatacciyar iska ke haddasawa. (Maryam)