in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tattauna kan batun kare hakkin bil Adam karo na 18 tsakanin Sin da Amurka
2013-08-03 16:54:29 cri
A ranar Laraba 31 ga watan Yuli da ta gabata, an yi taron tattauna kan batun kare hakkin bil Adam karo na 18 tsakanin kasashen Sin da Amurka a birnin Kunming dake kudu maso yammacin kasar Sin.

A yayin taron, bangaren Sin ya nuna cewa, tattaunawar da ake yi tsakanin Sin da Amurka tana da muhimmanci sosai ga kokarin bunkasa sabuwar hulda tsakanin kasaitattun kasashe. Sabili da haka, bangaren Sin a duk lokacin da ake tattaunawa kan batu ya kan bayyana cewa, ya kamata bangarorin biyu su bi ka'idojin girmama juna, zaman tare cikin lumana, da kuma daina tsoma baki kan harkokin cikin gida na kowane bangare. Bugu da kari, yana fatan bangarorin biyu za su warware dukkan sabani iri daban daban dake kasancewa a tsakaninsu kamar yadda ya kamata, ta yadda za a iya bayar da gudummawa ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka lami lafiya.

Haka kuma, bangaren Sin ya jaddada cewa, halin da ake ciki a kasar Sin wajen kare hakkin dan Adam ya fi kyau a tarihin kasar, kuma jama'a suna jin dadin hakkinsu kamar yadda ya kamata. Har ila yau bangaren Sin ya ki yarda da bangaren Amurka ya yi amfani da wasu matsalolin manyan laifuffuka domin tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasar Sin. Tana fatan bangaren Amurka ya girmama ikon shari'a na kasar Sin kamar yadda ya kamata, kuma ya daina yin amfani da irin wadannan matsalolin manyan laifufuka da suka auku a kasar Sin.

A nasa bangaren kuma, bangaren Amurka ya yaba ci gaban da kasar Sin ta samu wajen bunkasa tattalin arziki, zaman al'umma da kuma fama da talauci. A ganin bangarorin biyu, sun yi kokari sosai wajen tattaunawa kan batun kare bil Adam daga fannoni daban daban a fili, inda irin wannan tattaunawa ta taka rawa sosai wajen kara samun fahimtar juna tsakaninsu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China