A cewar Mista Hong, kasar Sin sam ba ta yarda da yin amfani da makamai masu guba ba ,tana kuma ganin cewa, idan har an tabbatar da cewa wani ya yi amfani da makaman, to, sai a yanke masa hukunci. A halin yanzu kasar Sin tana goyon bayan tawagar bincike ta MDD wadda a ganinta za ta gudanar da binciken yadda ya kamata don bayyana gaskiya da adalci. Sa'an nan kuma inji shi, kamata ya yi, a bar kwamitin sulhun majalisar ya yanke shawarar matakan da za a dauka bisa sakamakon binciken da za a samu. A ganin kasar Sin, daukar matakan soja na radin kai ta sabawa dokokin kasa da kasa, wadda kuma za ta kara sarkakiyar batun Sham, da haddasa tashin hankali a yankin da kasar ke ciki. Bisa la'akari da yanayin da ake ciki, a cewar Mista Hong, kasar Sin take kira ga bangarorin da batun ya shafa da su natsu tare da yin hakuri, sannan su nace don ganin an warware matsalar ta hanyar siyasa. (Bello Wang)