A cikin wata sanarwa, shugaban kungiyar ECOWAS, kuma shugaban tarayyar Najeriya, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa, tarayyar Afrika gaba daya tana tir da Allah wadai da duk wani lamarin da zai maida hannun agogo baya a kasar dake yammacin Afrika.
Mista Jonathan ya nuna cewa, ECOWAS za ta dauki duk wani matakin da ya wajaba ga duk wani yunkurin cigaba a kasar Guinea-Bissau da zai kawo barazana mai muni ga zaman lafiya da tsaro a yankin yammancin Afrika baki daya.
Ya kimanta wannan lamari da abun assha, tare da cewa babu wasu manyan dalilan aikata hakan a cikin wannan kasa.
"Sai dai kuma bayanai na nuna cewa wannan matsala ba za ta rasa halaka da boren neman karin albashi da kuma sabanin ra'ayi dake tsakanin sojojin kasar ba", in ji mista Jonathan.
Haka kuma ya soki wannan lamari da kakkausar murya da ya zo a lokacin da shugaban kasar da aka zaba Bacai Sanha wanda a yanzu haka yake birnin Paris na kasar Faransa domin samun jiyya.
Shugaban tarrayar Najeriya ya ja hankalin al'umma da sojojin Guinea-Bissau bisa girmama yarjejeniyar ECOWAS kan dimokaradiya da mulki na gari dake haramta duk wani sauyin gwamnati da bai bisa tsarin dokokin mulkin kasa. (Maman Ada)