"Ga abun da ya shafi kasata, duk da aiki tare da wasu abkilolin nahiyar Afrika, kasar Congo tun daga bakin shekarar 2002 ta kafa wani shirin kasa domin samar da manyan gine gine a cikin kasa bisa maida hankali kan fannonin da suka shafi sufurin kasa, sama da na ruwa, sarrafawa da rarraba makamashi, sarrafawa da rarraba ruwan sha masu tsabta tare da harkokin sadarwa. Bisa wannan yunkuri ne, kasarmu sannnu a hankali ta kebe a tsawon karnin da ya gabata muhimmin aikin samar da manyan gine gine", in ji shugaba Denis Sassou N'Guesso.
A lokacin da yake jawabi a yayin bikin bude dandalin tattalin arziki na shekara shekara na mujallar Forbes Afrika, mista Sassou ya jaddada cewa wannan kokarin zuba kudi da ya samu tallafi daga abokan huldar kasar Congo ya taimaka wajen gina hanyar motoci kilomita dubu daya, fiye da kilomita dari takwas na layin wutar lantarki, kilomita dubu daya na layin internet, tashoshin samar da makamashi da madatsun ruwa dake samar da karfin wuta na Megawatt 500, injunonin sarrafawa da tsare tsaren samar da ruwan sha masu tsabta. (Maman Ada)