Shugaba Xi Jinping ya kuma bayyana cewa, ya kamata a mai da hankali kan dangantakar da ke tsakanin yin gyare-gyare, neman bunkasuwa da kuma tabbatar da kwaciyar hankali, don ci gaba da 'yantar da tunanimmu, raya karfin samar da kayayyakin zaman takewar al'umma da kuma karfafa ayyukan kirkire-kirkire.
Shugaban kwamiti mai ba da shawara na kwalejin koyon ilimin gudanar da harkokin tattalin arziki na jami'ar Qinghua, kuma shugaban kamfanin Carlyle David M.Rubenstein da kuma shugaban majalisar cibiyar nazari ta Brookings na birnin Washington John L.Thornton sun ba da jawabi yayin ganawarsu da Mr. Xi, inda suka nuna imani cewa, kasar Sin na da kyakkyawar makoma, don haka, suna son ci gaba da karfafa ayyukansu a Sin, ta yadda za su ba da gudumawa ga bunkasuwar tattalin arziki da ayyukan ba da ilimi a kasar. (Maryam)