in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Belgium, 'dodo mai launin ja' a nahiyar Turai
2013-11-01 16:16:08 cri

Hakika dalilin da ya sa kungiyar ta farfado shi ne, wata manufar raya wasan kwallon kafa da kasar ta fara dauka a shekaru 10 da suka gabata. A wannan lokaci hukumar wasan kwallon kafan kasar ta fara kafa makarantun koyon fasahar buga kwallo a jihohin kasar, inda aka kebe karin lokaci domin ba da horo a fannin wasan kwallon kafa. Ta haka, yara masu tsananin sha'awar wasan kwallon kafa suka samu damar samun horo na sa'o'i 20 a ko wane mako, ba tare da yin watsi da koyon sauran sassan ilimi ba. Yanzu wasu daga cikin yaran da suka shiga makarantun a baya bayan nan sun riga sun zama fitattun 'yan wasan kwallon. Ga misali Kompany dan shekaru 27 a duniya, ya kasance daya daga cikin yaran. Ya kuma fara samun horo yana da shekaru 6 da haihuwa, har zuwa lokacin da ya kai shekaru 20 a duniya, ya ci gaba da karatu da buga kwallo karkashin tsarin kulob din Anderlecht. Kafin ya shiga Manchester City a shekarar 2008, ya riga samu digiri a wata jami'ar dake Belgium. Kana a shekarar 2012, ya fara koyon ilimin kasuwanci wato MBA, a wata kwalejin dake Manchester a kasar Birtaniya.

Hakika wannan tsari na tallafawa matasa samun damar karatu gami da horaswa a fannin wasan kwallon kafa ba zai iya rabuwa da kudi ba. Ga misali a farkon shekarar 2003, ko wace jihar kasar Belgium ta kan ware kudi har Euro miliyan 5 a ko wace shekara, don tallafawa kuloflika, ta yadda za su kara horar da yara. Sa'an na wasu kuloflika masu kudi su ma, su kan ware makuden kudi a wannan fanni, alal misali Standard Liege ta ware Euro miliyan 18 a shekarar 2012, don horar da 'yan wasa matasa. Ta wannan tsari ne aka samu damar samar da kwararrun 'yan wasa da yawa a kasar ta Belgium.

Ban da ware kudi da yawa don kara horar da 'yan wasa matasa, kasar Belgium ta yi amfani da kuloflika na sauran kasashen dake makwabtaka da ita don horar da matasanta. Idan mun kalli taswirar nahiyar Turai, za mu san dabarar Belgium tana da muhimmanci, domin ta makwabci Holland, Jamus, da Faransa, wadanda dukkansu suka kasance manyan kasashe a fannin wasan kwallon kafa. A da Belgium ta taba zama karkashin mallakar sarkin Holland, don haka kasashen 2 na da alaka sosai. Shi ya sa 'yan wasan kasar Belgium da yawa ke taka kwallo a Holland, ga misali Thomas Vermaelen da Jan Vertonghen, dukkansu, sun taba taka kwallo a Ajax a matsayin 'yan wasa matasa, inda suka samu kwarewa sosai. Kasar Farasa ita ma ta taimakawa Belgium wajen horar da matasa kan fasahar buga kwallon kafa. Ga misali Eden Hazard, an haife shi a birnin La Louvière, inda ake amfani da yaren Faransanci. Kuma kasancewarsa ya iya Faransanci, kuma garinsa na haihuwa na dab da birnin Lille na kasar Faransa, shi ya sa ya samu damar shiga kulob din Lille yayin da yake da shekaru 14 a duniya, kulob da ya shahara sosai a fannin horar da matasan 'yan wasa. Bayan da ya kwashe shekaru 7 yana samun horo a can, Eden ya zama wani tauraro a kulof din kasar Belgium. An ce cikin 'yan wasa taurari na kasar Belgium, rabinsu sun taba samun horo a Holland, kana kaso 2 daga cikin 10 sun fara tasowa ne a Faransa, yayin da sauran kaso 3 suka samu horaswa a kasarsu ta Belgium, inda aka fi samun kuloflikan da suka kware, wajen horar da 'yan wasa a kewayen birnin Brussels dake tsakiyar kasar.

Bisa kwashe shekaru 10 tana daukar matakan horar da karin matasa masu neman kwarewa a fannin wasan kwallon kafa, kasar Belgium ta daga daga matsayinta a jadawalin jerin kungiyoyin kasashen duniya, daga matsayi na 71, zuwa na 6. Wannan kadai zai sa mu gane cewa, muddin dai an dauki matakan samar da daidaito, ko shakka babu za a samu damar kafa wata kungiyar wasan kwallon kafa mai karfi a duniya. (Bello Wang)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China