130912DavosAmina.m4a
|
An bude dandalin tattauna kan tattalin arziki na Davos a lokacin zafi karo na 7 a birnin Dalian na kasar Sin a ran 11 ga wata, Firaminstan kasar Sin Li Keqiang da ya halarci taron a jawabin sa ya nuna cewa, yanzu Sin na cikin wani muhimmin lokaci na karkata hanyar samun bunkasuwar tattalin arzikinta, kuma tana samun bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata, har ma za ta shiga wani lokaci na daban wajen samun bunkasuwa mai inganci.
An yi wannan taro ne yayin da Sin ta nuna sanyi jikinta na saurin bunkasuwar tattalin arziki. Taron da ya samu halartar mutane sama da 2000, yawancinsu suna tambaya game da makomar tattalin arzikin kasar Sin. Shi ya sa, Mr Li Keqiang ya tabbatar a bayaninsa cewa:
"Ina son gaya muku cewa, Sin na fuskantar wani muhimmin lokaci ne wajen karkata hanyar da za ta bi ta samun bunkasuwar tattalin arziki, yanzu haka, tattalin arzikin kasar na samun bunkasuwa yadda ya kamata. Babbar ka'ida da muke dauka ita ce samun bunkasuwa mai dorewa, har ma mu dauki wasu matakai na kirkire-kirkire, sannan mu ba da kulawa ga dukkan fannoni, kyautata tsare-tsare, sa kaimi ga kwaskwarima da ake yi da kuma ba da tabbaci ga samun bunkasuwa lami lafiya."
Mr Li yana mai cewa, duk da matsalar da Sin take fuskanta ta koma bayan tattalin arziki, gwamnati za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace wajen daidaita harkokin tattalin arziki daga manyan fannoni, tare kuma da tsayawa tsayin daka kan hana karuwar gibin kasafin kudi, tare kuma da daukar matakin kudi da ya dace, ban da haka za ta goyon bayi sha'anoni masu samar da kayayyaki. Dadin dadawa, za ta nace ga manufar bude kofa ga kasashen waje tare kuma da nazarin sabuwar hanyar da ta dace a wannan fanni. Mr Li ya bayyana cewa:
"Bisa halin da ake ciki a watannin Yuli da na Agusta, ma'aunin PMI da PPI da dai sauran ma'aunai mafi muhimmanci a fannin tattalin arziki sun samu karuwa, yayin da sha'anonin samar da kayayyaki suka samu bunkasuwa yadda ya kamata, ban da haka, an samar da karin aikin yi a birane da garuruwa, farashin kayayyaki ya yi daidai, sannan kuma kasuwanni suke samun bunkasuwa yadda ya kamata, abin da ya bayyana makoma mai kyau a fannin tattalin arzikin kasar Sin a nan gaba. Saboda haka, babu shakka, burin da aka yi a gaba zai cika."
Mr Li Keqiang a jawabin sa ya furta cewa, yanzu Sin ta shiga mataki na sauya hanyar raya tattalin arziki, saboda haka saurin karuwar tattalin arziki ya ragu kuma ya yi daidai bisa tsarin da aka tsayar. Ban da haka, ya jaddada cewa, ya kamata, Sin ta samu bunkasuwa mai inganci nan gaba tare da yin tsimin makamashi da kiyaye muhalli, dole ne a mai da hankali kan sha'anin kirkire-kirkire da kimiyya da fasahohi, har ma ba da tabbaci ga samar da guraben aikin yi da daga kudin shiga na jama'a. Ban da haka, Mr Li ya jaddada cewa:
"An yi kiyasin cewa, yawan kayayyaki da Sin za ta shigo da su daga kasashen waje a cikin shekaru biyar masu zuwa zai kai dala biliyan 10,000, kuma yawan kudin da Sin za ta zubawa kasashen ketare zai kai dala biliyan 500, jimlar mutane da za su yi yawon shakatawa a kasashen waje za ta kai kimanin miliyan 400. Sin na fatan hadin kai da sauran kasashe domin yin amfani da wannan zarafi mai kyau, kuma tana fatan kasa da kasa za su samar da yanayi mai kyau wajen yin hadin gwiwa tsakaninsu da Sin."
Ban da haka, Li Keqiang ya bayyana cewa, Sin kuwa na fatan shiga aikin daidaita harkokin kasa da kasa tare kuma da samar da karin kayayyaki, har ma da yin musayar ra'ayi tare da kasashe masu tasowa kan kawar da talauci da ba da gudumawarta a wannan fanni. A matsayin wata kasa mai tasowa, yawan mutane da suka fama da talauci a kasar Sin ya kai kimanin miliyan 100, hakan ya sa, ya kamata Sin ta dauki nauyi na kasa da kasa dake bisa wuyansa yadda ya kamata bisa halin da take ciki. Dadin dadawa, Firaminista Li Keqiang ya yi kira ga kasashe daban-daban da su mai da hankali kan zurfafa tsarin bude kofa tare kuma da yaki da manufar ba da kariya. Ya kuma bayyana cewa, Sin kuwa na maraba da jarin da kamfanonin kasashen waje za su zubawa nan kasar Sin, da kuma daidaita yanayin zuba jari da ba da tabbaci ga ikon mallakar fasaha.
Shugaban dandali Klaus Schwab a cikin jawabinsa na bude taron, ya nuna imaninsa cewa, tattalin arzikin kasar Sin za ta zama wani mataki mai muhimmanci wajen sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, kuma Sin za ta samu nasara kan kwaskwarima da take yi na karkata hanyar raya tattalin arziki. (Amina)