in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na iya tabbatar da samun dauwamammen cigaban tattalin arzikinta
2013-09-11 16:41:59 cri
Jiya Talata a birnin Dalian na kasar Sin, firaministan kasar Li Keqiang ya gana da ma'aikatan masana'antu na gida da na kasashen ketare, dake halartar taron dandalin tattaunawa na Davos na yanayin zafi na bana.

Wannan ne dai karo na farko da Li Keqiang ya halarci taron shekara shekarar a matsayinsa na firaministan kasar Sin. Yayin kuma da yake amsa tambayoyin wakilan ma'aikatan masana'antun kasashen ketare, Li Keqiang ya bayyana cewa, ko da yake kasar Sin za ta fuskanci kalubale, wajen samun bunkasuwar tattalin arzikinta a nan gaba, amma tana da karfi, da ikon gudanar da sharuddan tabbatar da samun dauwamammen ci gaban tattalin arziki yadda ya kamata.

Don gane da karin bayani kan wannan batu, ga sharhin da abokiyar aikimmu Bilkisu ta hada mana.

Taron tattaunawa da aka shirya tsakanin firaministan kasar Sin da wakilan ma'aikatan masana'antun a wannan karo, muhimmin sashe ne na taron shekara-shekara, na dandalin tattaunawar Davos a yanayin zafi, inda kafofin watsa labaru ke iya samun muhimman bayanai game da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a nan gaba. Kamar dai yadda aka saba gabatarwa a ko wane karo.

"tun daga shekarar 2013, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya soma raguwa sannu a hankali, wannan ya janyo damuwar da kasashen duniya ke yi kan makomar tattalin arzikin kasar cikin dogon lokaci. Ko mene ne ra'ayinka kan wannan batu?"

Wannan ne tambayar da Giuseppe Recchi, babban daraktan kamfanin Eni na kasar Italiya ya bayar, wadda ta nuna damuwar kafofin watsa labaru na kasa da kasa kan makomar bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a nan gaba. Firaminista Li ya ba da sahihiyar amsa cewa, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya ragu sakamakon dalilai na ciki da na kasashen waje. A wannan yanayin da kasar ke ciki na fuskantar matsalar tabarbarewar tattalin arziki, ta yadda kasar Sin ba ta samu zarafin kyautata manyan manufofin ta na tattalin arziki, da kara gibin cinikayya, da kuma sassauta manufar kudi ba, a maimakon haka, ta zabi wasu hanyoyin na daban da take bi.

"hanyar da muke bi ita ce, tabbatar da zaman karko, da gudanar da manufofi a dukkan fannoni. Musamman ma taka muhimmiyar rawa da manufar yin gyare-gyare, da inganta kasuwa, da kyautatta tsarin tattalin arziki, da kuma canza hanyar bunkasuwa. Ya zuwa yanzu, an riga an gano amfaninsu."

Har ila yau, firaminista Li Keqiang yace, ba a kammala yunkurin kafa masana'antu, da giggina kananan garuruwa a kasar ta Sin ba, kuma kasar Sin na da makoma mai haske a nan gaba, wajen biyan bukatun gida. Yace ta hanyar amfani da nasarorin da aka samu sakamakon yin gyare-gyare, na iya inganta kasuwa cikin dogon lokaci. A sa'i daya kuma, tsarin tattalin arzikin kasar Sin na fuskantar matsalolin rashin daidaito, da karancin samun ci gaba mai dorewa. Saboda haka, har zuwa yanzu kyautatta tsarin tattalin arziki na kasancewa muhimmin aiki dake gaban kasar. Li ya kara da cewa,

"kyautatta tsarin tattalin arziki muhimmin aiki ne a wuyammu, wanda zai kuma taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da makomar bunkasuwa a nan gaba. Ta wannan hanya ce za mu iya karfafa ingancin karuwar tattalin arziki da kuma amfaninta, hakan za a iya taimaka wa jama'a wajen kara samun kudin shiga, tare kuma da inganta sayen kayayyaki."

Bayan haka kuma, Li Keqiang ya ce, kasar Sin na samun bunkasuwa ta fuskar ba da tabbaci, da kyauttata zaman rayuwar jama'a, tare da samar da guraban aikin yi, wanda dorewar hakan muhimmin kalubale ne dake gaban kasar. Don haka yace kasar Sin za ta dauki matakan da suka dace, wajen kara bunkasa sashen ba da hidima, tare kuma da bayar da horo game da sana'o'in da suka dace da manufofin samar da guraban aikin yi. A sa'i daya kuma, za a yi kokarin tabbatar da adalci ta fuskar samar da aikin yi, da canja ra'ayin jama'a na neman aikin yi. Li Keqiang ya ce,

"A kan kai ga samun guraban ayyukan yi masu gamsarwa ne, idan aka fara daga matsayi aiki na kasa. Ina iya gaya muku cewa, ni manomi ne a shekarun baya. Fasahohin da na samu yayin da nake manomi sun ba ni taimako sosai waje gudanar da aikin firaminista a yanzu."

Bugu da kari, Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi niyyar inganta kwaskwarima a manufofin kudi, da yin amfani da kudin ruwa a kasuwa, da samun ci gaban kasuwar jarin hada-hadar kudade, tare da kara bude kofa a gida, da ma kasashen ketare ta fuskar hada-hadar kudade. Kamar yadda aka saba, kasar Sin za ta ci gaba da samar da muhalli mai kyau ga kamfanonin kasashen ketare, domin samun damar zuba jari, da raya sana'o'insu yadda ya kamata.

Game da batun gurbata muhalli da kasar Sin ke fuskanta a yanzu, wanda kuma ke jawo hankalin kasashen duniya, Li Keqiang ya nuna cewa,

"kamata ya yi gwamnatin kasar Sin ta fidda tsayin da zai samar da ci gaba ta fuskar kiyaye muhalli. A sa'i daya kuma, ta dauki matakai masu nagarta na warware matsalar gurbatar muhalli da take fuskanta a yanzu. Za a kara kokari a fannonin samar da iskar gas, da tsaftacaccen ruwa, da kare kasa, tare kuma da kawar da masana'antu masu wanzar da ci baya." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China