Dokar a cewar gwamnan jihar ta Edo Adams Oshiomhole, ta biyo bayan gyaran fuskar da akaiwa dokar haramta yin garkuwa da mutane ta shekarar 2009 ne. Gwamna Oshiomhole ya ce wannan doka ta tanaji hukunci kisa ga wanda ya aikata, ko ya taimakawa masu garkuwa da mutane ta ko wace irin hanya.
Yace an kafa wannan doka ne duk kuwa da tarin kalubalolin dake tattare da aiwatar da ita, domin dakile mummunar sana'ar sace mutane dake ciwa al'ummar jihar tuwo a kwarya.
Daga nan sai Oshiomhole ya yi kira da matasan jihar da su kauracewa wannan mummunar sana'a, wadda a cewar sa ba zata taba zama halastacciyar hanyar neman arziki ba.(Saminu Alhassan Usman)