Shugaban Nigeriya Goodluck Jonathan a ranar Litinin 14 ga wata ya ce, gwamnatinsa ta gama shirye-shiryen da ya kamata domin tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Mali kafin nan da karshen mako mai zuwa.
Shugaban wanda ya furta hakan a lokacin wani liyafar da aka shirya ma jami'ai na jakadancin kasar a fadar gwamnatin dake Abuja, ya ce, ya kamata kasashe su hada kansu wajen yin alawadai da duk wani nau'in ta'addanci domin ba zai yiwu su mika kowane sashi na duniyar nan ga masu tsattsauran ra'ayi ba.
Ya ce, "Muna fuskantar wani yanayi yanzu haka a Mali. Bari in tabbatar maku da ma sauran kasashen duniya cewa, a matsayinmu na kasa za mu yi iyakacin kokarinmu na aiki tare don ganin an warware matsalar da ke faruwa a kasar." Sannan ya kara da cewa. "Masu sa ido a kan matsalar sun riga sun isa kasar ta Mali, don haka namu sojojin kiyaye zaman lafiyan za su isa kasar kafin karshen mako mai zuwa."
Shugaba Jonathan ya yi bayanin cewa, ko shakka babu a matsayin Nigeriya na mamban kungiyar tarayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, zai halarci taron da za'a yi kwanan nan, kuma yana sa ran zuwa mako mai zuwa dukkannin kasashen kungiyar da suka yi alkawarin tura sosojin kiyaye zaman lafiya za su aika da nasu domin taimaka ma sojojin Malin wajen 'yantar da kasar.(Fatimah)