in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukunta a Najeriya na tattaunawa da wasu kusoshin kungiyar Boko Haram
2013-10-09 09:46:16 cri

A Najeriya, ana ci gaba da tattaunawa tsakanin mambobin kwamitin lalubo hanyoyin sulhu da farfado da yanayin zaman lafiya na gwamnatin kasar, da wasu kusoshin kungiyar nan ta Boko Haram.

Tattaunawar dake daf da kamala, a cewar ministan ayyuka na musamman, kuma shugaban kwamitin da gwamnatin ta kafa Alhaji Kabiru Turaki, na da manufar kawo karshen zub da jini dake wakana sakamakon ayyukan kungiyar ta Boko Haram, musamman a yankunan arewacin kasar.

Turaki, wanda ya bayyana hakan jiya Talata yayin wani taron manema labarai a Abuja, babban birnin tarayyar kasar, ya kara da cewa, nan da dan lokaci za a kammala, tare da mika rahoton kwamitin ga fadar gwamnatin kasar.

A cikin watan Afirilun da ya gabata ne dai fadar gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa kwamitin lalubo hanyoyin sulhu, da gabatar da shirin yafiya mai kunshe da mambobi 26, wanda kawo yanzu ake ganin aikinsa bai kai ga haifar da wani sauyi game da halin da ake ciki ba.

A baya dai mutumin dake ikirarin shugabancin kungiyar Sheik Abubakar Shekau, ya taba yin watsi da batun afuwar da aka ce za a yi wa 'ya'yan kungiyarsa, kasancewar a cewarsa, ba su aikata wani laifi da za su bukaci afuwa ko yafiya ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China