Wani babban jami'in sojan Najeriya ya bayyana a ranar Jumma'a cewa, cibiyar sojojin Najeriya da ke horas da aikin wanzar da zaman lafiya, ta horas da dakaru kusan 810 wadanda za a tura aikin wanzar da zaman lafiya yankin Darfur na kasar Sudan.
Kwamandan cibiyar, Salihu Uba, ya bayyana a bikin yaye dakarun da aka yi a bataliya ta 342 da ke Jaji a arewa maso tsakiyar Najeriya cewa, cikin wadanda aka horas din, sun hada da jami'ai 43 da sauran masu mukamai 767.
Uba ya ce, bataliyar ta kwashe makonni 4 tana horas da dakarun ne, ta yadda za su kimtsa tunkarar aikin wanzar da zaman lafiya na MDD, don ganin sun tafiyar da aikin yadda ya kamata a yankin na Darfur, kana ya yi na'am da halayyar da sojojin suka nuna yayin samun wannan horo.
Jami'in ya ce, ba ya shakkun cewa, za su nuna irin wadannan kyawawan dabi'u yayin da suke gudanar da aikin nasu. (Ibrahim)