in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojoji a Najeriya sun hallaka wasu mahara 30
2013-10-08 10:44:28 cri

Rundunar sojoji a tarayyar Najeriya ta ce, ta hallaka wasu mayakan kungiyar nan ta Boko Haram su 30, sakamakon wani sumamen da jami'anta suka gudanar a wasu sansanonin 'ya'yan kungiyar dake jihar Borno.

Mataimakin kakakin runduna ta 7, ta sojin kasar kaftin Aliyu Danja ne ya tabbatar da hakan ga manema labaru a jiya Litinin. Danja ya ce, jami'an rundunar sojin sun samu nasarar harbe maharan su 30 ne, yayin da suke kokarin tserewa daga kauyen Damboa, bayan sun hallaka wasu al'ummar kauyen su 5 da safiyar ranar Asabar 5 ga wata.

A ci gaba da daukar matakan dakile ayyukan kungiyar ta Boko Haram da rundunar ke gudanarwa, Danja ya ce, ko da a ranar Lahadin da ta gabata ma sai da dakarunta suka kai wasu hare-hare ta sama da kasa, kan sansanin maharan dake garin Izza, bayan da rundunar ta samu sahihin labarin shirin maharan na kaiwa garin Bama hari.

Ya ce, yayin farmakin na ranar Lahadi, dakarun rundunar sun lalata motoci, da kayayyakin yakin da maharan kungiyar ke amfani da su.

Hare-hare daga mayakan kungiyar ta Boko Haram dai na dada karuwa, musamman a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, jihar da ke da iyaka da kasashen Kamaru, da Nijar, da Chadi, lamarin da ake danganta shi da tasirin kungiyoyin tada kayar baya kamar Aqim, mai alaka da Al-Qaida, dake da sansani a arewacin Afirka. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China