A ranar Talata 15 ga wata ne rundunar sojan Najeriya ta tabbatar da cewa, ta halaka mayakan 'yan kungiyar nan ta Boko Haram 40 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Kakakin rundunar sojan Aliyu Danja ya bayyana cewa, dakarun runduna ta 7 ta sojojin Najeriya sun dakile wani yunkurin da 'yan kungiyar suka yi na kaddamar da wasu hare-haren ta'addanci da suka shirya kaiwa a lokacin bukukuwan Sallah a garuruwan Bama, Gwoza da Pulka.
Jami'in ya ce, sojojin sun yi nasarar dakile hare-haren da 'yan kungiyar suka shirya kaiwa, inda suka kashe 'yan ta'adda 40 a garuruwan guda 3, yayin da wasu da dama suka tsere da raunin harbin bindiga.
Bugu da kari, Danja ya ce, sojojin sun lalata wata mota kirar a kori-kura makare da abubuwan fashewa da aka yi nufin tarwatsa garin Bama da su.
A cewarsa, sojojin sama na Najeriya sun hada kai da dakarun kasa na rundunar sojan a harin da suka kai na musamman kan 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram da kayayyakinsu, harin da ya ce, ya yi nasara. (Ibrahim)