A ranar Jumma'a ce 19 ga wata, wakilin musamman na MDD a kasar kwadibwa Boert Koenders ya yi kira da a gudanar da zaben yankuna da gundumomi da za'a gabatar ranar Lahadi lami lafiya kuma cikin adalci, inji mai magana da yawun magakatardan MDD Martin Nesirky yayin bayani ga 'yan jarida.
A cikin sakonsa ga al'ummar duniya baki daya, Koenders ya lura da cewa, an samu rahotanni na hayaniya a yayin gangamin 'yakin neman zabe, don haka yake kira ga masu ruwa da tsaki dasu nuna halayya da ya dace don tabbatar da gudanar da zaben ba tare da rikici ba.
Sakamakon hakan, hukumar MDD a kasar kwadibwa (UNOCI) za ta sa ido sosai kan yadda abubuwa ke gudana dangane da zaben a birnin Abidjan da ma sauran sassan kasar.
Rahotanni na baya bayan nan daga MDD na mai yabawa kasar dangane da ci gaba da ta samu a fuskar tsaro, shekaru biyu bayan fuskantar tashin hankali bayan zabe a kasar dake yammacin Afirka.
Mataimakin magatakardan MDD a fuskar aikin kawo zaman lafiya Edmond Mulet ya bayyana a baya cikin wannan mako cewa, kasar kwadibwa ta samu ci gaba tun barkewar rikicin bayan zabe, kuma ta shiga wani sabon shafi da kara inganta zaman lafiya, to amma ta fuskanci 'yan matsaloli da rashin daidaito a wasu sassan yammacin kasar dake da iyaka da kasar Libya.
Irin wadannan rikici na nuna yanayi na yiwuwar rikici kuma alamu ne dake nuna cewa, har yanzu kasar kwadibwa tana fuskantar barazana dake bukatar a shawo kansu don a tabbatar da dorewarta, inji Mulet.
A ranar 21 ga watan Afrilu ne za'a yi zabukan yankuna da na gundumomi a kasar kwadibwa. Masu lura da lamura suna kira da a yi zabe cikin kwanciyar hankali musamman ma bayan fuskantar wasu tashe-tashen hankula a lokacin yakin neman zabe. END