Shugban ya mai da hankali kan yadda aka gudanar da zaben a ranar 11 ga watan Disamba da ya gabata, inda ya nuna babban sha'awa ga zaben.
Jean Ping ya ce, wannan zaben wani sabon mataki ne da zai tabbatar da cikakken sassan jamhuriyar kuma wata hanya ce ta karfafa ci gaban dimokradiyya.
Daga nan shugaban ya yi kira ga duk wadanda suka shiga takarar da su rungumi duk sakamakon da yan kasar suka zaba, kazalika in har suna da korafi da su bi dokar da aka shimfida wajen neman hakki.
Daga karshe Jean Ping ya alkawarta cewa kungiyar ta AU za ta ci gaba da baiwa al'ummar Cote d'Ivoire goyon baya tare da karfafawa shugabannin kasar gwiwa wajen tabbatar da dimokuradiyya da hadin kan kasar baki daya.(SALAMATU)