Ministar dake kula da sufurin jiragen sama, madam Stella Oduah ta bayyana cewa an gano akwatin nadar bayanai na wannan jirgi. Jirgin sumfurin Embraer 120, mai lambar 5N-BIT dake karkashin kamfanin Associated Airlines ya tarwatse jim kadan bayan tashinsa na harkar kasuwanci daga Lagos zuwa Akure. An nuna cewa jirgin saman na dauke da kusan mutane 20 idan aka hada da masu tukin jirgin, tare kuma da gawar tsohon gwamnan Olusegun Agagu na jihar Ondo dake kudu maso yammacin Najeriya.
Madam Oduah ta nuna cewa akwatin nadar bayyanan an mika shi hannun cibiyar bincike da rigakafin hadura domin gano dalilin abkuwar wannan hadari.
Shugaban majalisar sanatocin Najeriya ya bayyana cewa hukumarsa ta jajantawa iyalan wadanda wannan hadari ya rutsa da su, haka shi shugaban 'yan majalisar dokokin Najeriya Aminu Tambuwal ya kimanta wannan hadari da abu mafi muni tare da yin kira ga 'yan Najeriya da su bada nasu taimako da goyon bayansu a cikin wannan lokaci na juyayi. (Maman Ada)