Mai magana da yawun hukumar ta NEMA Ibrahim Farinloye, ya tabbatarwa Xinhua cewa,an gano gawawwaki 9 a wurin da hadarin ya faru,yayin da mutane 6 suka ritsa da rayukansu
Wata sanarwa da Xinhua ta samu ta ruwaito,janar manajan hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Lagos(LASEMA) Femi Oke-Osanyintolu na cewa, mutane 11 ne suka mutu a hadarin kana mutane 4 suka ritsa da rayukansu
Wasu majiyoyin hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman kasar, sun bayyana cewa,jirgin yana dauke da gawar tsohon gwamnan jihar Ondo ne Olusegun Agagu a kan hanyarsa ta zuwa Akure, babba birnin jihar, kafin ya fadi a Lagos.
Kakakin hukumar ta NEMA,ya bayyana cewa, hukumar na gudanar da bincike game da musabbabin hadarin. (Ibrahim)