1007murtala.m4a
|
Al'ummar musulmi a Najeriya za su yi bikin babbar salla tare da 'yan uwansu musulmai a duk fadin duniya a ranar 15 ga watan Oktoba.
Sarkin musulmin kuma shugaban majalisar sha'anin musulunci ta kasa, Alhaji Sa'ad Abubakar ya sanar da hakan a jiya Lahadi a fadarsa dake Sokoto.
Ya yi bayanin cewa ranar Arfa na wannan shekara ta kama ranar 14 ga watan Oktoba, don haka babbar salla wato sallar layya za ta kama kashegari ranar 15 ga watan Oktoban.
Ana sa ran gwamnatin tarayyar Najeriya za ta sanar da ranar Talata 15 ga wata a matsayin ranar hutun babbar salla, da karin kwana daya ko ranar Litinin 14 ko ranar Laraba 16 ga wata ya zama shi ma ranar hutu. (Murtala Zhang)