Bisa sakamakon zaben da hukumar zaben kasar ta Guinea mai zaman kansa ta bayar, an ce, jam'iyyar kawancen jama'ar Guinea ta RPG da ke karkashin jagorancin shugaban kasar mai ci Alpha Conde, ta samu kujeru 53 daga cikin 114 da ke majalisar dokokin, yayin da jam'iyyar da ta kafa kawance tare da ita ta samu kujeru 6, don haka bisa jimilla kawancen jam'iyyun ya samu kujeru 59.
A hannu guda kuma babbar jam'iyyar 'yan hamayya ta UFDG ta samu kujeru 37, sai kuma sauran jam'iyyun adawa da suka samu kujeru 15, wanda hakan ke nuna cewa daukacin 'yan hamayyar sun samu kujeru 52 kenan. Wannan kididdiga ta nuna cewa kawancen jam'iyyun da ke mulkin kasar ya dara jam'iyyun 'yan hamayya da yawan kujeru 7 a majalisar dokokin kasar.
Tuni shugaban hukumar zabe na kasar ta Guinea mai zaman kanta ya bayyana cewa, za a mika sakamakon zaben a hannun kotun kolin kasar, wadda za ta yanke hukunci, ta kuma sanar da sakamakon.
A wannan rana kuma, kawancen jam'iyyun 'yan hamayya ya bayyana kin amincewarsa da sakamakon zaben, inda kakakinsa ya ce, sakamakon zaben bai nuna hakikanin ra'ayin jama'ar kasar ta Guinea ba.
Kafin wannan kuma, tawagar sa ido ta kasa da kasa da ke kunshe da wakilan MDD, da wakilan kungiyar Tarayyar Turai ta EU, da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS, da jami'an diplomasiyya na kasashen Amurka da Faransa, ta bayyana cewa, an saba ka'idojin zabe, an kuma yi almundahana a wasu yankuna yayin zaben, matakin da ya sanya aka gaza kidaya kuri'u da dama a wasu wurare.(Tasallah)