in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardan MDD ya nuna gamsuwa dangane da batun zabe a Guinea
2013-07-05 10:14:58 cri

A ranar Alhamis, magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya yi maraba da rattaba hannu da aka yi kan yarjejeniya da aka kulla tsakanin bangaren shugaban kasa da na jam'iyyun 'yan adawa a kasar Guinea game da batun tsarin gudanar da zaben majalisa a kasar.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunnsa ya bayar, Mr. Ban ya ce, ya gamsu matuka da wannan nasara da aka cimma, wacce ta zamo wata shimfidar gabatar da zaben majalisa lami lafiya kuma cikin adalci.

An fara tattaunawar ne tsakanin bangarorin siyasa tun wasu watanni da suka gabata, inda aka samu karkare yarjejeniyar siyasa da aka rattaba hannu kanta ranar Laraba a Conakry, babban birnin kasar, tsakanin manyan kusoshi dake adawa da juna kan batun siyasa.

Wadanda aka yi zaman tattaunawar ta siyasa sun amince a gudanar da zaben 'yan majalisa da aka jinkirta na tsawon lokaci, a cikin watan Satumba mai zuwa, kana a tabbatar da cewa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar (CENI) tana aiki yadda ya kamata.

Ya kamata a gudanar da zaben 'yan majalisa a kasar Guinea watanni shida bayan zaben shugaban kasa wato cikin watan Nuwamban 2010, domin a samu kawo karshen rikici da ya barke sakamakon juyin mulkin soja da aka yi a watan Disamban 2008.

To amma hakan bai samu yiwuwa ba saboda banbance-banbance da tashin hankali tsakanin jam'iyyu dake adawa da juna. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China