in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta tallafa wa zabubukan da za'a shirya a Guinea-Bissau
2013-08-20 14:13:36 cri

Kasar Sin za ta ba da taimako domin ganin an gudanar da zabubukan ranar 24 ga watan Nuwamba mai zuwa a kasar Guinea-Bissau, in ji jakadan kasar Sin dake Bissau, mista Wang Hua ba tare da ba da jimillar kudin wannan tallafi ba, jakadan, bayan ya yi wata ganawa da shugaban hukumar zaben kasar, Augusto Mendes, ya jaddada niyyar jama'ar kasar Sin wajen taimakawa tabbatar da tsarin demokaradiya, har ma da cigaban kasar Guinea-Bissau.

Mista Wang Hua ya kuma bayyana cewa, ganawarsa tare da mista Mendes ta ba shi damar sanin halin da ake ciki game da shirye shiryen wadannan zabubuka na shugaban kasa da na 'yan majalisu.

Hukumar zaben kasar ta bayyana bukatarta na neman kudin Euro miliyan 5,5 domin gudanar da wadannan zabubuka yadda ya kamata.

A yayin da ita kuma cibiyar tallafawa gudanar da zabe, wata hukumar da aka baiwa nauyin yin rajistan masu zabe ta gabatar da kasafin aikinta na kudin Sefa biliyan bakwai kwatankwacin dalar Amurka miliyan goma sha hudu.

Amma har zuwa yanzu, abokan kasar dake goyon bayan wannan zabe a kasar Guinee-Bissau, kamar kungiyar EU, MDD da kungiyar ECOWAS ba su fitar da kudaden gudanar da zabubukan ranar 24 ga watan Nuwamba ba.

Sai dai wakilin musammun na sakatare janar na MDD, Jose Ramos Horta ya ba da sanarwa a cikin watan Junin da ya gabata cewa, akwai sauran miliyan uku na Euro na cikin kudin da aka kebe na zaben shugaban kasa na shekarar 2012 da ba'a cimma nasarar shirya ba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China