in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa sabuwar gwamnatin hadin gwiwa a Guinee-Bissau
2013-06-08 14:42:51 cri

An gabatar da wata sabuwar gwamnati ta hadin gwiwa da aka kafa a ranar Alhamis da yamma a kasar Guinee-Bissau, bayan makonni na shawarwari tsakanin manyan jami'an siyasa na kasar bisa matsin lamba na gamayyar kasashen duniya, a wani labari na hukumomin kasar a ranar Alhamis.

Sabuwar gwamnatin na kunshe da mambobi 34 da duka hada da ministoci 19, sakataren kasa 15, da a cikinsu akwai mata hudu. Abu mafi muhimmanci shi ne shigowar jami'an PAIGC, jam'iyyar dake yawan 'yan majalisa 67 bisa 100 a majalisar dokoki. Wannan jam'iyya dake kan iko kafin juyin mulkin ranar 12 ga watan Afrilu, ta ki yarda da shiga gwamnatin hadin gwiwa da bukatar dawowar shugabanninta da sojoji suka kora kamar tsohon firaministan kasar Carlos Gomez Junior da kuma Raimundo Pereira, tsohon makadashin shugaban kasa.

Kafa wannan sabuwar gwamnati ta bude kofar mataki na biyu na mulkin wucin gadi na maido tsarin mulki yadda ya kamata, da zai kare watanni shida bayan shirya zabubuka.

Yarjejeniyar da aka cimma a ranar 17 ga watan Mayu tsakanin manyan jam'iyyun siyasa na kasar, jam'iyyar PAIGC da jam'iyyar PRS mai 'yan majalisa 28 a karkashin jagorancin kungiyar tarayyar Afrika AU da MDD ta taimaka wajen kafa wannan sabuwar gwamnatin hadin gwiwa a kasar Guinee-Bissau. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China