Gwamnatin kasar Guinee-Conakry ta nuna fargabenta kan kira da wasu manyan kusoshin jam'iyyun adawar kasar suka yi na kafa wani kwamitin kare kai domin kiyaye tsaron lafiyar jama'a da dukiyoyinsu a cikin unguwannin birnin Conakry da aka fi yawan samun tashe-tashen hankali, duk da cewa, akwai jami'an tsaron dake nauyin kare lafiyar jama'a da dukiyoyinsu suke sintiri a wadannan unguwanni, a cewar wata sanarwa da hukumomin kasar suka fitar a ranar Lahadi.
A cewar wannan takarda, wadannan kiraye kiraye na kwamitocin 'yan banga sun samu yaduwa ta wasu kafofin watsa labarai na kasar, da nuna goyon baya ga wannan hali na shiga boren kasa. Gwamnatin kasar ta lura cikin bakin ciki cewa, tun ranar 21 ga watan Mayu, ranar jana'izar wasu magoya bayan gungun 'yan adawa, zuwa jerin gwano na ranar 22 ga watan Mayu da kuma shirya ranar matattar kasa a ranar 23 ga watan Mayu, tashe-tashen hankali sun cigaba da bazuwa da kuma kamari a wasu manyan unguwannin birnin Conakry, musammun ma bisa hanyar Bambeto zuwa Coza. Sanarwar ta kara da cewa, an samu asarar rayukan jama'a da asarar dukiyoyin jama'a, kuma cin zarafin mutane ya zama ruwan dare a wadannan wurare, don haka kafa wasu kwamitocin 'yan banga zai kasance wani abun fargaba da tashin hankali.
Saboda wannan mataki na 'yan adawa ya kaucewa kundin tsarin mulki, shi ya sa gwamnatin kasar ta dauki niyyar amfani da duk wasu matakan da suka wajaba na ganin za su kawo karshen wadannan tashe-tashen hankali domin maido da zaman lafiya da tsaro da kuma murkushe duk wani bore. (Maman Ada)