Tattaunawa da ke tsakanin jam'iyyun kasar Guinea tun 'yan watanni da suka gabata ta fara samun nasara, inda aka sa hannu kan wata yarjejeniya tsakanin manyan masu adawa wadanda ake damawa da su a tsarin siyasar kasar.
Mai shiga tsakani na kasa da kasa Said Djinnit shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa bayan ganawa da aka yi ranar Talata a birnin Conakry.
Wadanda aka yi zaman tattaunawar da su sun amince a bar 'yan kasar Guinea dake wajen kasar su jefa kuri'a a zaben kasar mai zuwa na majalisa da kuma gudanuwar hukumar zaben kasar (CENI) yadda ya kamata.
Djinnit ya bayyana cewa, jam'iyyar shugaban kasar, ta 'yan adawa da jam'iyyun tsakiya duka sun amince da abin da ke kunshe cikin yarjejeniyar.
A madadin wadanda suka shirya taron da al'ummar duniya baki daya, Djinnit ya yaba nasarar da aka cimma da kuma amincewa da hakan da aka samu tsakanin bangaren shugaban kasar da jam'iyyun adawa.
Ya ce, ya kamata 'yan kasar Guinea baki daya su yi farin ciki game da kammala tattaunawar ta siyasa cikin nasara.
Ya ci gaba da cewa, saboda wannan tattaunawa, yanzu jam'iyyun za su iya gabatar da yarjejeniya ga kasar ta yammacin Afirka, wacce za ta bude kofar tabbatar da gaskiya, shigowar sauran bangarori da kuma gabatar da zabe cikin adalci.
Mai magana da yawun 'yan adawa, Aboubacar Sylla ya ce, ya gamsu da abin da tattaunawar ta haifar tare da ba da karin tabbacin cewa, 'yan adawa za su shiga shirin zaben.
Don kammala tattaunawar da yarjejeniyar, masu shirya taron sun sake kiran wani zaman ganawa ranar Laraba tsakanin 'yan siyasa, wakilan hukumar zaben kasar, abokan hulda da kuma wakilan bangaren jakadanci a Guinea. (Lami)