A ranar Alhamis 17 ga wata ne, babban zauren MDD ya zabi kasashen Chadi, Chile, Lithuania, Najeriya da Saudiyya don zama sabbin mambobin kwamitin sulhu na MDD na tsawon shekaru biyu, yayin wata kuri'a da aka kada a asirce.
Shugaban babban taron na wannan karo John William Ashe ne ya bayyana hakan, yana mai cewa, sabbin mambobin za su fara aiki ne a ranar 1 ga watan Janairun shekara ta 2014, inda za su maye gurbin kasashen Azerbaijan, Guatemala, Morocco, Pakistan da Togo.
Ko da ya ke kasashen Chadi, Saudiyya da Lithuania ba su taba zama mambaobin kwamitin sulhun ba, yayin da Najeriya da Chile dukkansu sun taba kasancewa a kwamitin sulhun har sau 4 a baya.
Bisa dokokin MDD, sai kasa ta samu kashi 2 bisa 3 na kuri'un mambobin babban zauren na MDD mai wakilai 193, ko kuma kuri'u 129. Kana babban zauren MDD ne ke zabar mambobin kwamitin da ba su da kujerun din-din-din a kwamitin sulhun su guda 10, inda ake zabar kasashe biyar a watan Oktoban ko wace shekara.
Sauran ragowar kasashe biyar masu kujerun din-din-din a kwamitin sulhun na MDD su ne kasashen Burtaniya, Sin, Faransa, Rasha da kuma Amurka, kasashen da aka dora musu alhakin kula da harkokin zaman lafiya da tsaro a duniya.(Ibrahim)