in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru sun yaba da zabar Najeriya cikin kwamitin sulhu na MDD
2013-10-18 10:51:09 cri

Kwararru kan hulda da kasashen waje a Najeriya, sun yaba da yadda aka zabi kasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka cikin kwamitin sulhu na MDD na tsawon wa'adin shekaru biyu.

Wani masani kan kimiyyar siyasa da dangantakar kasa da kasa a jami'ar Abuja da ke Najeriya mai suna Saleh Dauda, ya fada a ranar Alhamis cewa, zabar kasar ta Najeriya, wata alama ce da ke nuna komawar kasar kan harkokin kasa da kasa a matsayinta na mai karfin fada a ji a nahiyar Afirka.

Ya ce, 'Ko da yake zabar kasar ta Najeriya cikin kwamitin sulhun na MDD ba zai warware matsalar cikin gidan kasar ba, amma zai inganta harkokin cikin gidan kasar tare da kara martabar 'yan Najeriya dake kasashen waje.'

Bugu da kari, zabar Najeriya a kwamitin sulhun, wata dama ce ta bayyana matsalar da nahiyar ke fuskanta da nufin samun tallafin kasashen duniya game da batutuwa kamar kwararowar hamada, cutar kanjamau, zazzabin cizon sauro, shugabanci na gari, batun ayyukan 'yan ta'adda da sauransu.

Shi ma tsohon jakadan kasar Najeriya a kasar Saudiyya, Magaji Mohammed, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, zaben Najeriya cikin kwamitin sulhun, zai kara fito da martabar kasar, kasar za ta kara taka rawa a harkokin tsaro na kasashen duniya. Sannan wata dama ce ta kara samun masu sha'awar zuba jari a kasar.

Idan ba a manta ba, a shekara ta 2011, shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya bayyana shirin kafa wata hukumar sasanta rigingimu a ofishin babban sakataren MDD, da nufin bullo da dabarun warware rigingimu a sassa daban-daban na duniya.

A jawabinsa yayin babban taron MDD karo na 66, shugaba Jonathan ya ce, aikin hukumar shi ne tattara bayanai game da rigingimu, gano sassan da abin ya shafa, kana a tsara hanyoyin warware su bisa adalci. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China