in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya ce, samar da tsarin samar da abinci mai dorewa shi ne makamin kawo karshen yunwa
2013-10-17 10:57:53 cri

A ranar Laraba 16 ga wata ne babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, samar da isasshen abinci da kulawa da fito da tsari mai dorewa na kula da abinci shi kansa, su ne muhimman hanyoyin kawo karshen yunwar da ake fuskanta a duniya.

Ban Ki-Moon ya bayyana hakan ne cikin sakon da ya aika a bikin ranar samar da abinci ta duniya, inda ya ce, a kowa ce ranar, akwai mutane sama da miliyan 840 da ke fama da yunwa, adadin da ya ce kamata ya yi a dauki matakin da ya dace don magance shi.

Ya ce, hanya daya tilo ta samar da abinci mai gina jiki da tabbatar da cewa ko wane mutum ya samu abincin da ya kamata, ya godara ne ga kyawawan matakan samar da abinci, manufofi da matakan zuba jari a bangaren samar da abinci, jama'a su kansu, hukumomi, muhalli, hanyoyin samar da amfanin gona, yadda ake sarrafa su, da yadda suke isa ga jama'a ta hanyoyin da suka dace kuma masu dorewa.

A cewar alkaluman MDD, baya ga mutane miliyan 840 da ke fama da yunwa mai tsanani, akwai karin mutane miliyan 2 da ke fama da karancin abubuwa masu jina jiki da ake bukata don kasancewa cikin koshin lafiya.

Taken bikin ranar samar da abinci ta duniya na wannan shekara, wanda aka yi bikin a ranar Laraba 16 ga wata don karrama ranar da aka kafa kungiyar samar da abinci da aikin gona ta MDD (FAO) a shekara ta 1945 shi ne, 'tsarin samar da abinci mai dorewa don tsaron abinci da ingancinsa'. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China