in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta mai da hankali ga yanayin siyasar Sudan ta Kudu
2013-07-25 09:56:53 cri
Tawagar MDD dake kasar Sudan ta Kudu ko UNMISS a takaice na nazarin irin halin da siyasar kasar ta tsinduma, bayan da a baya-bayan nan shugaban kasar Salva Kiir ya tsige mataimakinsa Riek Machar daga mukaminsa, ya kuma bayyana rushe gwamnatin, tare da dakatar da jami'i mai shiga tsakanin kasar da makwafciyarta Sudan.

Da yake karin haske dangane da wannan lamari, mataimakin kakakin MDD Eduardo del Buey ya ce, tuni hambararren mataimakin shugaban kasar ya amince da rushe gwamnatin da aka yi, yana mai tabbatar da ikon da shugaba Kiir ke da shi na daukar wannan mataki, ko da yake ya ce, a shirye yake ya kalubalanci hakan yayin zabukan kasar na nan gaba.

Kawo yanzu dai a cewar wannan mataimakin kakakin MDD, babu wani, ko wata kungiya da ta nuna haramcin daukar wannan mataki na shugaba Kiir, bisa tanajin kokokin kasar ta Sudan ta Kudu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China