in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD zai kira taron Geneva karo na 2 kan kasar Syria
2013-10-18 10:44:10 cri

Kakakin MDD Martin Nesirky, ya fada a ranar Alhamis 17 ga wata yayin taron manema labarai cewa, babban sakataren MDD Ban Ki-moon, zai kira taron Geveva karo na biyu game da kasar Syria.

Nesirky ya ce, Ban Ki-moon yana kokarin ganin an gudanar da taron na Geneva a tsakiyar watan Nuwamba, inda za a gayyaci dukkan bangarorin da abin ya shafa domin su halarta.

Manufar taron da aka shirya gudanarwa, ita ce, dorawa kan abubuwan da aka tattauna a taron da ya gabata a baya wanda aka yi a karshen watan Yunin shekarar 2012 a Geneva, inda taron ya bukaci sassan da ke gwabza fada da juna a Syria, da su hanzarta tsagaita bude wuta, kana a bullo da kafar sasantawa da nufin kafa gwamnatin wucin gadi.

Bugu da kari, kakakin na MDD ya ce, wakilin musamman game da kasar ta Syria Lakhdar Brahimi, zai yi tattaki zuwa Syria don tattaunawa da kososhin sassan da taron ya shafa.

A cewar Nesirky, ko za a gayyaci kasar Iran ko a'a a taron, wannan zai kasance daya daga cikin abubuwan da za a tattauna a ganawar tasa. Amma jami'an MDD sun fada tun farko cewa, yana da muhimmanci Iran ta halarci taron. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China