Wata sanarwa da kungiyar haramta amfani da makamai masu guba a duniya (OPCW) ta bayar ranar Laraba 16 ga wata, ta bayyana cewa, an kafa wata tawagar hadin gwiwa tsakanin kungiyar ta OPCW da MDD.
Sanarwar ta kuma bayyana nada Sigrid Kaag a matsayin jami'in gudanarwa na tawagar OPCW da MDD na musamman, tawagar da aka kafa da nufin hanzarta lalata makamai masu guba da kasar Syria ta mallaka ta hanyar da ta dace, inda tawagar ta bayyana kudurinta na ci gaba da aikin da tuni tawagar kungiyar OPCW da MDD suka fara gudanarwa a kasar ta Syria.
Bugu da kari, sanarwar ta ce, ko da a ranar Laraba, kungiyar OPCW da MDD kowane ya kaddamar da wata gidauniya a hekwatocinsu wadanda za su rika tallafawa juna.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, ya zuwa ranar Laraba da safe, tawagar hadin gwiwar ta gudanar da aikin tantance wasu wuraren ajiye makamai masu guba na kasar ta Syria guda 11. Kana a ranar Talata, kungiyar ta OPCW ta ce, an kara karfin tawagar ta masu aikin share fage da MDD da wasu rukunoni masu bincike na kungiyar da karin ma'aikatan MDD, inda yanzu yawan ma'aikatan tawagar hadin gwiwar ya kai 60.
Bayanai na nuna cewa, a ranar 6 ga watan Oktoba ne rukunin farko na masu aikin binciken makamai masu guban ya fara aikinsa, kuma yanzu haka tagawar da ke aikin share fagen ta yi nisa wajen nazarin bayanan da gwamnatin Syria ta gabatar game da shirin makamanta masu guba.
Kwamitin sulhu na MDD ya bayyana cewa, kungiyar haramta amfani da makamai masu guba ta duniya(OPCW) za ta taimakawa kasar Syria wajen ganin an lalata makamanta masu guba ya zuwa tsakiyar shekara ta 2014.
Ana sa ran kara karfin tawagar da yawan masu aikin bincike, wadanda ake sa ran za su isa kasar ta Syria da yaki ya warzaga a ranar 1 ga watan Nuwamba. (Ibrahim)