Kungiyar ba da agaji ta kasa da kasa ta Red Cross wadda cibiyarta a birnin Geneva take ta tabbatar a ranar Lahadi cewa, an sace ma'aikatanta guda shida tare da wani mambanta, 'dan asalin Syria a birnin Idlib dake arewa maso yammacin kasar Syria. 'Har yanzu ba'a da wata masaniya kan mutanen da suka sace su, mutane ne da ke dauke da makamai da ba'a fayyace su ba.' in ji wata sanarwa.
Ma'aikatan masu aikin agaji sun je Idlib domin kimanta bukatan kiwon lafiyar jama'a a wannan yanki da kuma magungunan da asibitocin wadannan wurare suke bukata, in ji sanarwar.
'Muna kira da a saki wadannan mutane cikin gaggawa ba tare da wani sharadi ba.' in ji madam Magne Barth, shugabar tawagar Red Cross a kasar Syria.
Kungiyar Red Cross ta kasa da kasa da kungiyar din da ke Syria na aiki tare wurjanjan ta fuskar jin kai ba tare da nuna son kai ba ga mutanen da suka fi kasancewa cikin bukata, in ji madam Barth tare da bayyana cewa, wannan hadari yana rage karfin ba da taimako ga jama'ar dake cikin bukata.
Red Cross ta lashi takobin kai taimako ga al'ummar Syria tare da cigaba da ayyukanta na jin kai a kasar, da ma sauran kasashen da ke makwabtaka da ita, inda aka tsugunar da 'yan gudun hijirar Syria. (Maman Ada)