in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya wani harin kunar bakin wake kan gidan talabijin na kasar Syria
2013-10-14 10:17:02 cri

Kamfanin dillancin labarai na kasar Syria ya bayar da rahoto a ranar Lahadi cewa, wasu 'yan kunar bakin wake sun tada wasu bama-baman da suka dana a cikin wasu kananan motocin da suka ajiye a kusa da ginin hedkwatar gidan talabijin na kasar da yammacin ranar Lahadi a Damascus, babban birnin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar lalacewar kayayyaki tare da katse shirye-shiryen da ake watsawa a tashar.

Gidan talabijin din ya bayyana cewa, an ajiye kananan motocin ne a nisan mita 20 daga fitilar baiwa ababan hawa hannu da ke daura da shingen hedkwatar gidan talabijin din daga hannun dama, lamarin da ya yi sanadiyar raunata wasu masu wucewa, an kuma gano wata gawa a wurin da fashewar ta abku, inda jami'ai suka yi imanin cewa, ita daya daga cikin wadanda suka dana bom din ne.

Bugu da kari, daga bisani gidan talabijin din ya nuna hotunan bidiyon lamarin da ya faru, inda ya nuna irin barnar da ta faru a dandalin Umayyad, tsakiyar birnin Damascus da hedkwatar sojojin Syria.

Harin na ranar Lahadi, ya faru ne sa'o'i bayan da dakarun 'yan adawa na FSA, wato kungiyoyin da ke dauke da makamai da ke adawa da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad suka bayyana cewa, za su warzaga Damascus, babban birnin kasar da makaman roka, muddin dakarun gwamnati suka ci gaba da kai hari kan yankunan da ke hannun 'yan tawaye. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China