A yayin ganawar, Li Keqiang ya ce, kasar Sin tana son hada kai da Uganda wajen zurfafa hadin gwiwar da ke tsakaninsu a fannonin ababan more rayuwar jama'a, makamashi, aikin gona da dai sauransu, da sabunta hanyoyin yin hadin gwiwa don kawo wa jama'ar kasashen 2 alheri.
Sa'an nan mista Li ya nuna cewa, raya hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka, wani muhimmin sashi ne a manufofin Sin a harkokinta na diplomasiyya, haka kuma wani tsayayyen zabi ne da kasar Sin ta yi bisa manyan tsare-tsare. Kamar yadda ta yi a baya, kasar Sin za ta ci gaba da mara wa kasashen Afirka baya da su karfafa karfinsu na tsayawa da kafafunsu, da kara azama kan kasashen duniya da su kara mai da hankali da zuba jari a nahiyar ta Afirka, a kokarin tabbatar da samun zaman lafiya da bunkasuwa da wadata a Afirka.
A nasa bangare, mista Mbabazi ya bayyana fatansa na ganin Uganda da Sin sun zurfafa huldar abokantaka a tsakaninsu, inganta yin mu'amala a tsakanin jam'iyyu, da habaka hadin gwiwa a fannoni daban daban, a kokarin kara raya dangantakar da ke tsakaninsu. (Tasallah)