A yayin gudanar da shirin, ban da birnin Beijing, biranen Guangzhou, Kunming, Changchun, Urumqi, Zhengzhou da sauran wurare su ma sun gudanar da shirin, inda masu aikin sa kai za su yi musayar bayanai da sauran jama'a game da matsalar yunwa. Bangaren da ke daukar nauyin shirin ya yi hasashe cewa, yawan mutane da za su halarta zai kai fiye da miliyan 30.
Bisa sabon rahoton da MDD ta gabatar, an ce, a halin yanzu akwai mutane kimanin miliyan 842 a duniya da suka dade suna fama da matsalar yunwa, kana yawan kananan yara wadanda yawan shekarunsu bai kai 5 ba da suka mutu sakamakon rashin abinci a kowace shekara ya kai miliyan 5.
"Kananan yara dake fama da matsalar yunwa da rashin abinci mai gina jiki za su fuskanci matsaloli da dama, ban da lafiyarsu, za su fuskanci matsaloli a makaranta har ma a wuraren aiki a nan gaba.", a cewar wakilin hukumar WFP dake kasar Sin Huang Ansheng. Kana ya kara da cewa, don warware matsalar, ana bukatar jama'a da su yi hadin gwiwa tare da shiga a dama da su don warware matsalar a duniya. (Zainab)