in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WFP ta kai agajin farko zuwa Mogadishu
2011-07-28 11:39:24 cri
A ranar Laraba da ta gabata, hukumar abinci ta duniya wato WFP ta fara kai agajin farko zuwa Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya, inda dubban mutane suke fama da fari a kudancin kasar, in ji mai magana da yawun hukumar.

Jirgin sama mai daukar agajin ya sauka a filin jirgin sama na Mogadishu. Wannan shi ne karo na farko da agaji daga hukumar WFP ya isa kasar ta Somaliya bayan shekara ta 2009 da 'yan tawaye masu tsattauran ra'ayin addinin Musulunci suka hana hukumomin agaji su gudanar da ayyuka a Somaliya.

Jirgin agajin ya dauke abinci mai gina jiki da yawansa ya kai ton 14 domin yara da suke fama da rashin abinci mai gina jiki a sansanonin 'yan gudun hijira da ke Mogadishu, kamar yadda mai magana da yawun sashen kula da harkokin Afrika ta tsakiya da gabashi na hukumar WFP, David Orr ya sanar.

Da yake shaida wa manema labarai a filin saukar jirage na Mogadishu, Orr ya ce, wasu agaji na nan tafe nan da 'yan kwanaki masu zuwa don ceto mutanen da ke fama da matsananciyar yunwa sakamakon farin da ya yi katutu a kasar. (Salamatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China