in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar WFP ta kafa wata hanyar jin kai a yammacin kasar Libya
2011-04-20 15:54:05 cri

Ranar Talata 19 ga wata a birnin Geneva, kakakin hukumar tsara shirin abinci ta duniya wato WFP Emilia Casella ta bayyana cewa, WFP ta kafa wata sabuwar hanyar jin kai a yammacin kasar Libya, wadda za ta yi amfani ga fararen hula dubu 50 a wannan yanki domin fitar da su daga kangin yunwa cikin wata daya mai zuwa.

Casella ta ce, hukumar WFP ta yi sufurin garin shimkafa ton 240 da biskit ton 9.1 daga Tunisya zuwa yammacin Libya wadanda za su biya bukatun mutane dubu 50 cikin wata daya.

Casella kuma ta ce, za a rarraba cimakar ga mata da kananan yara da farko, kuma wuraren da za a rarraba wannan cimaka sun hada da Tripoli babban birnin kasar da dai sauran kyauyukan dake kewayensa.

A wannan rana kuma, ministan harkokin waje na kasar Faransa Alain Juppe ya ce, ba za a yarda da turawa sojojin kasa zuwa Libya ba. Jami'in harkokin waje na kasar Birtaniya William Hague kuma ya ce, kasar za ta kara tura sojojinta zuwa yankin Benghazi na Libya domin tallafawa wasu 'yan tawaye. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China