WFP ta ba da sanarwa a wannan rana cewa, wadannan kasashe sun fuskanci bala'in fari a bana, abin da ya sa miliyan mutane su na fama da yunwa. WFP da hukuma mai kula da 'yan gudun hijira, suna fatan kasashen duniya da su kara samar da kudi domin sayen abinci ga wadannan kasashe.
WFP ta ce, alal misali, bala'in fari da aka fuskanta a kasar Nijar ya kawo illa ga aikin gona, abin da ya haifar da hauhawar farashin amfanin gona, har ma ana fuskantar karancin hatsi. Yawan jarirai da suke da watanni shida zuwa 23 da haifuwa na fama da karancin abinci mai gina jiki. A cikin watanni shida da suka gabata a bana, WFP ta samarwa 'yan kasar Nijar sama da miliyan 1 abinci, ban da wannan kuma, WFP na shirin ci gaba da samarwa kasar abinci daga watan Yuni zuwa na Satumba.
Dadin dadawa, WFP ta ce, jami'in hukumar da wani babban jami'in na hukumar 'yan gudun hijira ta MDD sun tafi kasar domin sa ido kan halin da ake ciki a kasar ta Nijar. Wadanda kuma, sun sa ido kan shirin da WFP ta yi kan jama'ar wurin na shiga aikin gine-ginen more rayuwa domin samun abinci.(Amina)