in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin HNA na kasar Sin ya ba da kudin Sin yuan miliyan 10 kyauta ga aikin kyautata abincin yara na kasar Ghana
2013-05-22 21:43:42 cri
A ranar 22 ga wata, hukumar tsara shirin samar da abinci ta kasa da kasa WFP ta majalisar dinkin duniya da kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Hainan na kasar Sin wato HNA suka kulla wata yarjejeniya, inda wannan kamfanin kasar Sin zai samar da kudin Sin yuan miliyan 10 ga hukumar, ta yadda hukumar za yi amfani da wadannan kudi wajen samar da abinci mai gina jiki ga kananan yara wadanda suke karatu a kasar Ghana. Sakamakon haka, kananan yara mata 3900 na kasar Ghana wadanda suke karatu za su iya samun abinci mai gina jikinsu a cikin shekara daya.

A yayin bikin kulla yarjejeniyar, Ertharin Cousin, babbar direktar hukumar WFP ta bayyana cewa, kasar Sin tana kasancewa daya daga cikin kasashe wadanda suka fi samun nasara wajen yin hadin gwiwa da hukumar WFP. Bisa yarjejeniyar da ta kulla da kamfanin HNA, kananan yara wadanda suke fama da yunwa yanzu za su ji dadin rayuwa sabo da abinci mai gina jiki da za a samar musu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China