in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yau ne ranar abinci ta duniya karo na 33
2013-10-16 10:53:34 cri
Yau Laraba 16 ga wata ita ce ranar abinci ta duniya karo na 33, kuma taken ranar na wannan shekara shi ne "koshin lafiyar jikin mutum ya dogara ga tsarin samar da abinci mai lafiya", ana sa lura kan raya tsarin samar da abinci mai dorewa da tabbatar da tsaron abinci da ingancinsa.

Don murnar ranar samar da abinci ta duniya karo na 33, an fara bikin makon abinci na duniya ne tun daga ranar 14 ga wata, inda ake yin tattaunawa kan wannan batu, da yin tsere da sauran bukukuwa domin yaki da yunwa. Kana a ranar 17 ga wata, hukumar shirin samar da abinci ta duniya wato WFP za ta gudanar da bikin munar wannan rana a cibiyarta dake birnin Rome.

Har yanzu ana fuskantar matsalar abinci a duniya, inda yunwa da tamowa suka kasance manyan matsalolin da dan Adam ke fama da su. Bisa rahoton da hukumar WFP ta gabatar, an ce, a halin yanzu akwai mutane kimanin miliyan 870 a duniya da ke fama da matsalar yunwa. Ko da yake matsalar ta ragu idan aka kwatanta da shekarar 2009, amma akwai gibi sosai a tsakanin burin rage rabin yawan mutanen da ke fama da yunwa a duniya a shekarar 2015 da MDD ta gabatar. Kana rahoton ya ce, saboda karuwar yawan mutane a duniya, yawan bukatar abinci a duniya a shekarar 2050 zai karu da kashi 60 cikin kashi dari bisa na yanzu, don haka ana fuskantar kalubale a wannan fanni.

Hakazalika kuma, bala'u da raguwar gonaki za su yi tasiri ga farashin kayan abinci a duniya. Sabo da haka, akwai jan aiki a gaban kasashen duniya wajen raya tsarin samar da abinci mai dorewa da kuma tabbatar da tsaron abincin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China