Magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya bayyana ranar Litini a birnin Genava cewa, an cimma wasu muhimman kudurorin muradun karni, don haka ya dace a kara himma don a samu karin nasara.
Magatakardan har ila yau ya kaddamar da rahoton muradun karni na shekarar 2013 yayin bukin bude taron majalisar tattalin arziki da zamantakewa ta MDD (ECOSOC), ta shekarar 2013.
Ban Ki-Moon ya yaba nasarori da aka cimma kan muradun karni, inda ya baiyana cewar, yawan mutane dake fama da matukar talauci ya ragu zuwa rabin adadin, domin a yanzu mutane sama da biliyan 2.1 suna samun ruwan sha mai kyau, kana an samu ci gaba matuka a yaki da cutar zazzabin cizon sauro, malariya da kuma tarin fuka.
Magatakardan har ila yau ya ja hankalin mahalartan zuwa sauran kalubale kamar na barazana ga dorewar muhalli, mutuwar yara 'yan kasa da shekaru biyar, da kuma take 'yancin mata da duka ke kunshe cikin rahoton, inda ya yi kiran a kara himma don a samu shawo kansu a dukkan shiyyoyi da kungiyoyi na al'umma. (Lami)