in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar M23 na nuna damuwa kan barazanar da al'ummar Goma ke fuskanta daga wasu dakaru
2012-12-20 10:49:22 cri

Babban reshen siyasa na kungiyar 'yan tawayen M23 a kasar RDC-Congo ya bayyana damuwarsa kan barazanar da kamari daga wasu dakarun kawo baraka kan fararen hula, da kuma jita jitar sake barkewar yaki, lamarin dake tura al'ummar birnin Goma daukar hanyar gudun hijira, a cewar wata sanarwar wannan kungiya da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kofinta a ranar Laraba.

"Tun yau da 'yan kwanaki, ake ta ganin shawagin dakarun kungiyar FDLR na kasar Ruwanda kan hanyar Bibwe zuwa birnin Goma." in ji wannan sanarwa, tare da jaddada cewa, a yanzu haka dakarun suna jibge a yankunan Karuba da Mushaki masu nisan kilomita 40 daga birnin Goma da suke jiran yi kawanya a cikin 'yan sa'o'i masu zuwa.

A cewar kungiyar M23, a ko ina akwai wadannan dakaru tare da sojojin gwamnati, kuma suna farautar mutanen da ba su iyar kare kansu bisa zargin cewa, suna marawa kungiyar M23.

'Yan tawayen M23 sun kwace birnin Goma a ranar 20 ga watan Nuwamban da ya gabata, daga baya kuma suka fice daga wannan birni bisa kiran shugabannin taron kasa da kasa kan yankin "Grands-Lacs" (CIRGL), bayan wani taronsu na ranar 24 ga watan Nuwamban da ya gabata a Kampala. Tawagar gwamnatin kasar Congo tare da tawagar 'yan tawayen M23 na cigaba da tattaunawa tun ranar 9 ga watan Disamban a birnin Kampala domin samar da hanyoyin da za su taimaka wajen kawo karshen rikici a gabashin RDC-Congo. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China