in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron shawarwari tsakanin gwamnatin Congo da 'yan tawayen M23 a Kampala
2012-12-10 11:18:46 cri

Tattaunawar neman kawo karshen yake-yake a gabashin kasar RDC-Congo sun fara gudana tun daga ranar Lahadi a birnin Kampala tsakanin gwamnatin Kinshasa da 'yan tawayen M23. Ministan harkokin wajen kasar Congo Raymond Tshibanda ke jagorantar tawagar gwamnatin kasar, a yayin da tawagar 'yan tawayen M23 take karkashin jagorancin sakataren zartaswa na kungiyar mista Francois Rucogoza.

Shugaban diplomasiyyar Congo ya bayyana a yayin bude shawarwarin cewa, ya iso Kampala tare da makasudi guda shi ne na kawo karshen tawaye a gabashin kasarsa.

Mista Rucogoza ya zargi gwamnatin Congo da aikata laifuffukan kisa da na kare dangi na kabilanci a wannan yanki, tare da nuna cewa, rashin shugabanci nagari na gwamnati ya sanya kasar RDC-Congo, kasa mai arzikin albarkatun ma'adinai cikin matsalar rashin cigaba.

Ministan tsaron kasar Ouganda, Crispus Kiyonga a matsayin mai sulhuntawa tsakanin bangarorin biyu, ya bayyana cewa, gamayyar kasa da kasa da wannan shiyyar na fatan ganin wadannan shawarwari na Kampala sun taimaka ga cimma hanyar warware rikicin gabashin kasar RDC-Congo.

Haka kuma ya gabatar wa gwamnatin Congo da 'yan tawayen M23 wata shawarar tattaunawa da za ta gudana a nan gaba a birnin Goma, babban birnin arwacin Kivu.

Shawarwarin sulhu tsakanin bangarorin biyu an fara shi ne cikin jinkiri na kwanaki biyu, dalilin jinkirin zuwan tawagar M23 a Kampala.(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China