Kakakin MDD Martin Nesirky ne ya bayyana hakan a taron manema labarai, inda tawagar ta MUNOSCO ta ce bayan musayar wuta tsakanin sassan biyu a karshen mako, yanzu bangarorin biyu suna amfani da kananan makamai kamar rokoki.
Tawagar ta MONUSCO ta kuma nanata kiran da ta yi na kai zuciya nesa kuma dakarunta da ke yankin na zaman shirin ko ta-kwana.
A ranar Jumma'a, kakakin MDD ya bayyana cewa, an dakatar da fada tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen kungiyar M23 a kusa da garin Kanyaruchinya, kimanin kilomita 15 daga Goma, babban birnin lardin arewacin Kivu.
Nesirky ya kuma bayyana cewa, MONUSCO ta girke dakarunta cikin shirin kota-kwana, tun lokacin da fadan ya barke a ranar 14 ga watan Yuli, kuma a shirye ta ke ta dauki dukkan matakan da suka dace, ciki har da amfani da karfi wajen kare fararen hula.(Ibrahim)




