in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Watakila akwai mutane 340 da suka riga mu gidan gaskiya a sanadin nitsewar wani jirgin ruwa a Tanzania
2011-09-10 20:41:47 cri

Gwamnatin kasar Tanzania a ranar 10 ga wata ta tabbatar da cewa, wani jirgin ruwa ya nitse a Juma'a 9 ga wata a wani wurin da ke tsakanin tsibirin Zanzibar da wani tsibiri na daban da ke dab da shi, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 340 daga cikin fasinjoji sama da 600 da ke cikin jirgin.

An kubutar da mutane sama da 250 da ke cikin jirgin, kana ana kokarin kai gawawwakin wadanda suka gamu da ajalinsu babban dandalin wasa na kasar, domin baiwa iyalansu damawar dubawa.

Yanzu haka, ana ci gaba da ayyukan ceto tare da bin bahasin hadarin.

An ce, wannan hadari shi ne mafi tsanani a tarihin Zanzibar.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China