Bisa labarin da aka bayar, an ce, a ranar 31 ga watan Mayu da dare, rukunin 'yan sandan teku na kasar Tunisiya ya samu labari cewa, yayin da wani jirgin ruwa dauke da 'yan gudun hijira ya kai zuwa wani wurin da ke da nisan kilomita 30 zuwa tsibirin Kerkenah, inda ya gamu da hadari, an ce, akasarin mutanen da ke cikin jirgin, 'yan kasashen Afrika ne da suka tsere daga yake-yaken kasar Libya, cikinsu har da mata da yara.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a wannan rana, yanayi a wurin ba ya da kyau, kuma 'yan gudun hijira sun yi wa jirgin yawa, lamarin da ya jawo nutsewar jirgin. Wannan jirgin ya yi ta bin ruwa a teku har ta tsawon kwanaki 5, yayin da mutanen da ke cikin jirgin suka yi ta kokarin shawo kan barazanar igiyar ruwa.(Bako)