A wannan rana, kakakin ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da takwaransa na ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin sun yi jawabai a game da sakamakon da cewa, abubuwan gaskiya da suka faru a shekaru kusan 4 da suka wuce sun shaida cewa, bunkasa dangantaka a tsakanin gabobi 2 na mashigin Taiwan yadda ya kamata, hanya ce mai dacewa, wadda ta samu goyon baya daga wajen dimbin jama'ar Taiwan. Cikin sahihanci ne ake fatan za a samu kwanciyar hankali a zaman al'ummar Taiwan yayin da mazauna wurin suke jin dadin zaman rayuwa. Babban yankin kasar Sin na son ci gaba da hada kai da sassa daban daban na Taiwan, a kokarin bude sabon shafi a fannin raya hulda a tsakanin gabobin 2 yadda ya kamata tare da farfado da al'ummomin Sinawa, bisa ka'idojin tsayawa tsayin daka kan kasancewar kasar Sin daya tak a duniya da kuma kin yarda da neman samun 'yancin kan Taiwan.
Bayan da ya samu nasara a zaben, Ma Ying-jeou ya ce, nan da shekaru 4 masu zuwa, za a ci gaba da zurfafa hulda a tsakanin gabobin 2 na mashigin Taiwan, inganta amincewa da juna a tsakaninsu, ta yadda za a kara samun jituwa a tsakaninsu, a maimakon samun matsala. (Tasallah)